Dandalin Siyasa

Dandalin Siyasa

Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
00:00
00:00

Rezumatul episodului

Shirin Dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya yi duba kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin cewa Hukumar Zaɓen Najeriye, ta gaza wallafa rajistar masu zaɓe a intanet cikin wa’adin da dokar Zaɓe ta tanada. Sai dai hukumar ta ce ba ta karya doka ba. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

Episoade

167-

Ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin INEC da saɓawa dokar zaɓe

Shirin Dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya yi duba kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin cewa Hukumar Zaɓen Najeriye, ta gaza wallafa rajistar masu zaɓe a intanet cikin wa’adin da dokar Zaɓe ta tanada. Sai dai hukumar ta ce ba ta karya doka ba. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

24 oct. 2026
166-

Jami'iyyar APC ta kaddamar da majalisar yaƙin neman ta a hukumance

Shirin dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali kan ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, da kuma martani akan zaɓen zaɓi jihar Kaduna a matsayin wurin fara gangamin Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

17 oct. 2026
165-

Shirin ragin kuɗin man fetur na wata 1 ya janyo cece-kuce a Najeriya

Shirin ‘Dandalin Siyasa’ tare da Michael Kuduson a wannan mako ya yi duba ne kan matakin gwamnatin Najeriya kan shirin samar da rangwamen farashin man fetur na tsawon kwanaki 30, da martanin ’yan adawa. Sannan za mu waiwayi hukuncin Kotun Ƙoli da kuma matsayin Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC, kan jam’iyyun siyasar da suka saɓa ƙa’idojin miƙa rajistar mambobinsu, da dai sauran batutuwan da muka tanadar muku a shirin. A daidai lokacin da ƴan Najeriya ke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, musamman farashin man fetur da sufuri, gwamnatin ƙasar ta sanar da wani mataki na rage nauyin da ke kan al’umma. Gwamnatin ta ce za a sayar da man fetur bisa rangwame a gidajen mai na kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC, na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu jigilar fasinjoji fifiko. Sai dai mataki bai burge ƴan adawa ba, domin kuwa sun mayar da martani, inda suke ke tambaya ko rangwamen na ɗan lokaci zai iya magance matsalolin da suka shafi tsadar rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakke shirin.

10 oct. 2026
164-

Jawabin Tinubu na cika shekaru 66 da samun ƴancin kan Najeriya ya bar baya da ƙura

Shirin ‘Dandalin Siyasa’ na wannan mako, ya maida hankali ne kan cikar Najeriya shekaru 66 da samun ƴancin kai, kuma yayin da ake bikin wannan rana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan ƙasar jawabi inda ya jaddada nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta ce ta samu a fannin tattalin arziki, tare da bayyana fatansa na ganin ƙasar ta samu ƙarin wadata. Sai dai shugaban bai yi magana kan matsalar tsaro da ke ci gaba da ta zame wa wasu sassan ƙasar ƙarfen ƙafa ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.............

03 oct. 2026
163-

A Najeriya shirin yaƙin neman zaben 2027 ya shiga wani sabon mataki

Shirin na wannan makon tare da Michael Kuduson, ya yi nazari ne akan yadda a Najeriya yakin neman zaben 2027 ya shiga wani sabon mataki, bayan fara yakin neman zaben kujerun gwamna da ’yan majalisun jihohi a hukumance, inda Hukumar zabe ta Najeriya INEC ta kuma tunatar da ’yan takara da jam’iyyun siyasa cewa dole ne su gudanar da yakin neman zabe bisa tanade-tanaden doka.

12 sep. 2026